Ali Nuhu da Adam A. Zango, ko kuma Sarki Ali da Prince Zango - kamar yadda aka fi sanin su a Kannywood - mutane ne masu matukar hazaka da kokari akan harkar fina-finan Hausa.
'Yan wasan na Kannywood na da magoya bayan da babu wani a masana'antar ya mallaka.
Sai dai ba magoya baya suka fi kowa kawai ba - sun fi kowanne dan wasan Kannywood yawan "munafukai" da ke kusa da su.
Watakila hakan ne ya sa suka fi ko wadanne 'yan wasan Kannywood yawan rikici a tsakaninsu.
Tambayar da kowa ke yi ita ce su wane ne wadannan mutane da ba sa so a zauna lafiya tsakanin fitattun jaruman na Kannywood? Kuma yaushe za su daina rikici tsakanin su?
Adam A. Zango, wanda ya wallafa wasu hotunansa a shafinsa na Instagram tare da Ali Nuhu ranar Asabar da daddare bayan sun kwashe wata da watanni suna "gaba", bai bayyana sunayen munafukan ba.
"Karshen munafukai...mai wuri ya dawo...Allah ina godiya da irin wadannan jarabtar da ka yi min," in ji Adam A. Zango.
Wannan shine take tabbatarda Shiri tsakaninmu Prince Zango da Sarki Ali.
Yanxu Kannywood take dawo guda daya, tsintsiya madaurinki daya.
A huta lapiya..


Post a Comment