Matasa 100 su ka Amfana da Tallafin Dan kasuwa a Keffi ta hanyar koyar da su sana'oin Hannu.
Hanshakin Dan kasuwanan na garin Keffi Alhaji Bala Ibrahim Mulki ya koyarda matasa kimanin dari daya sana’o’in hannu saboda dogaro da kai.
Dan kasuwan wanda ya durmaye harkan siyasa wanda a yanzu haka yake niman kujerar Dan Majalisar dokokin Jihar Nasarawa a mazaver Keffi ta gabas .a karkashin tutar Jami’iyyar APC.
Ya taimakawa matasa da aiyukan hannu domin rage radadin talauci. Da yake zanatawa da manema Labarai bayan tabbatar da samuwan wanan shirin na tallafin. Alhaji Bala Ibrahim Mulki mai kamfanin Dan Mulki Global Investment Nigeria Ltd. Yace ; a koda yaushe yanada burin tallafawa matasa saboda suna tushen cigaban kowata alumma.
Idan matasa suka samu abin dogaro da kafafunsu to alumma zata samu cigaba a kowata qasa.
Ya kara da cewa yana takaici idan an wayi gari yaga ga matasa amma basu da aikinyi. Yace; a Nijeriya Allah ya hore mana matasa masu hazaqa amma rashin tallafa masu yasanya muka zama koma baya.
Alhaji Bala Ibrahim Mulki wanda a yanzu haka yake takarar kujerar Dan Majalisa a Mazaver Keffi ta gabas.
Yace; idan Allah yasa yayi nasara zai kara bunkasa ire-iren wananan damar na koyar da matasa sana’o’in da zai iya rikesu domin dogaro da kai.
Abubuwan da za’a rikayi ba zai tsaya a garin Keffi bane kawai daga ko’ina za’arika shigowa Keffi ana sayan kayan , yace; wanan cigabane .
Yakara da cewa idan ya zama Dan Majalisa zai bada fifiko wajen kulawa da vangaren Ilumi da sana’a . idan mutum ya samu Ilumi yasan yadda zaiyi amfani da iluminsa.xan haka zaiyi kokarin fadada wanan cibiyar tazama na dindindin a mazaversa.
Cikin abubuwan da aka koyar da matasan sun hada da karatun Kwamfuta garana gashi , garean waya , aski, wankin mota na zamani da sauransu.
Bala Mulki yace; munanan daram akan bakanmu na niman wanan mukami saboda alumma suka bukaci mufito takara domin ganin cancantarmu .
Kuma zamuyi masu abubuwan da suka dace dasu idan muka lashe zave, saboda duk Soyayyan da zakayiwa wanda kakeso idan baka da katin zave babu yadda zakayi a ranar zave.
Bala Mulki yayi kiraga alumman mazaversa dana qaramar hukumar Keffi dama Jihar Nasarawa dasu fito kawai da kwarkwata su karbi katin zabe
Haka zalika ya yabawa Gwamnan Jihar Nasarawa Alhaji umar Tanko Al-makura bisa ga irin cigaban da ya samar a wanan jihar.sanan ya bukaci alumman Jihar dasubaiwa Gwamnan Jihar tare da Shugaban qasa goyon baya a zaven 2019.
Sanan ya bukaci alumma dasuyi komai cikin kwanciyar hankali da lumana siyasa zavine kowa yanada wanda yakeso domin ra’ayine kada ka tilastawa wani cewa saiyayi abinda kakeso.

Post a Comment