Tsananin saboda da danna wayar hannu musamman tun daga kananun shekaru na da matukar illa a cewar wani likita a Kano, Dakta Tijjani Haruna.
Eaya na haddasa raunin kakwalwa ta yadda za ka samu yaro ko matashi kwakwalwarsa ba ta ja ko fizge kamar yadda ya kamata a harkar karatu na boko ko na addini.
Wannan kuwa zai iya kasancewa ko da a ce mutum a baya kafin illar ta same shi yana da fahimta. Fahimtar na dakushewa a dalilin illar sab da waya da ya kama shi.
Haka kuma saboda wayaya na haddasa rashin barci. Da farko hakan na farawa ne daga mutum shi zai ke hana kansa barci saboda yana duba waya, daga baya kuma kwakwalwarsa za ta saba da wannan yanayi na tukura kai, ta yadda ko da mutum na son ya yi barci a kan lokaci musamman da daddare, sai barcin ya ki samuwa har sai lokacin da ya saba kwanciya.
Shi kansa karancin barci ba karamin lalaura bane domin dai ya na taruwa ya haddasawa kwakwalawa matsala ta rudewa da rashin kaifi da kuma yin nauyi matuka.
Likita Tijjani Haruna, wanda ke aiki da asibitin kwararru na Muhammadu Abdullahi Wase da ke a birnin Kano ya bayyanawa kamfanin dillacin labarai na Nijeriya a jiya Lahadi cewa, tsananin sabo da duba waya na haddasa cutar taiba (kiba maras misali) da kuma takure natsuwa da tunani.
Likitan ya yi kira da iyay a gida da makarantu da su dauki mataki mai tsauri wajen hana yara fara amfani da waya tun suna da kananun shekaru don gudu hanasu kamuwa da tsananin sabo da ita.
Wasu iyaye a Kano sun koa kan yadda matasa suka yi mummunar sabo da manyan wayoyi na zama ta yadda za ka matashi na duba waya ko yana daddana waya har a kan hanya, kamarin da iayaen suka bayyana a matsayin lalura mai matukar hadari ga matsan.

Post a Comment