Jam`iyyar APC reshen karamar hukumar Buji tayi kira ga masu kafa kuru`a a yankin su tabbatar sun zabi yan`takarar da zasu kawo cigaban yankin a babban zaben 2019 dake tafe.
Shugaban jam`iyyar APC na yankin, Alhaji Umar Nuhu yayi wannan kiran a lokacin dan`majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Birnin kudu da Buji, Injiniya Magaji Da`u Aliyu ya ziyarci kauyen Dankoshe domin duba aikin hanyar burji da ta tashi daga Kwanar Bakarawa zuwa Dankoshe.
Ya yabawa dan`majalisar bisa kokarinsa na kawo ribar dimokradiyya ga alummar yankin.
A nasa jawabin Injiniya Magaji Da`u Aliyu, yace hanyar mai tsawon kilomiya goma-sha biyu ana gudanar da aikinta ne akan kudi naira miliyan goma sha hudu a karkashin ayyukan mazabu na tarayya.
Daga nan yayi akawarin cigaba da samar da ribar dimokradiyya ga alummar mazabarsa, inda ya bukaci su sake zabensa a shekara ta 2019.
Alummata.com

Post a Comment