Kungiyar kiristocin Nijeirya (CAN) ta gargadi shugabanin ‘yan siyasa a kan yin amfani da matasa wajen haddasa rikicin siyasa, ya kamata su yi amfani da su ne wajen raya kasa.

Kungiyar a yayin da ta bayyana hakan ta ce caji matasan Nijeriya da su kasance masu kishin kasa, da hazaka ida har suna so su zanto wani abu a kasar musamman ma wannan lokacin da kasar ke fuskantar matsaloli da dama.

A yayin da ya ke magana a taron nada sabbin shugaban matasa na kungiyar CAN ta kasa  (YUWICAN) a ranar Juma’a a birnin tarayya Abuja, shugaban kungiyar CAN, Rev Dr Samson Olasupo Ayokunle, ya ce babbar matsalar rashin samun aikin yi a kasar Nijeriya duk da basirarrun matasan da kasar ke da su shine rashin shugabanni masu basira tare da yadda ‘yan siyasa ke amfani da matasa domin cimma kudirorinsu.

Ya ce, “An kusa gudanar da zaben 2019, an fara yakin zabe. Ina mai kira ga ‘yan siyasa da daina amfani da matasa wajen haddasa rikicin siyasa tare da magudi. Allah ya ba mu matasa masu basira ne domin mu yi amfani da su wajen raya kasar nan.

“Ya kamata ‘yan siyasa su daina amfani da su wajen haddasa rikice-rikice. Ina kira ga matasan Nijeriya musamman Kiristoci da su kauracewa duk wani rikice-rikice da magudin zabe.”


Post a Comment

 
Top