
Wata gobarar da aka kasa gano tushenta ta kama wani garejin bakanike inda ta kona motoci 19 da ke ajiye a ciki.
Wannan lamari ya faru ne a yankin Awada da ke garin Onitsha a jahar Anambra da misalin karfe 2:00 na daren yau Juma’a.
Mai magana da yawun ‘yan sandan jahar, SP Haruna Mohammed ya fadawa jaridar Daily Post cewa wasu daga cikin motocin sun kone kurmus yayin da wasu suka kone kadan.
Post a Comment