To kamar haka ne kuma bai kamata mu ja baki mu yi shiru a cikin maganar yadda aure ya dena dadi yanzu ba. Domin abu ne idan an bar shi a hakan zai iya zarcewa daga kanmu har kan na bayanmu.
Abu mafi muhimmanci kuwa shi ne, bayan mun yi tambayar mu nemo amsa ko amsoshin. Sannan bayan mun nemo amsoshin mu yi aiki. Wato mu yi kokarin sauya abin da zai sauyu, mu debe abin da dama tarkace ne kawai ba shi da wani amfani.
Mu kuma shigo da manda muka ki shigo da shi, alhalin mun san shigo da shi din shi zai fi taimakon mu. Sannan mu dawo da wanda a baya yana ciki mu ka dauke shi, tare da cewa mun tabbata yana taimaka mana a cikin tafiyar.
Muna rokon Allah Ya katarshe mu zakulo abubuwan da za su amfane mu baki daya. Ga wasu daga cikin amsoshin tambayoyi:
1. Wannan Ya Kamata In Ajawai
Zabi shi ne mataki na farko, kuma mafi muhimmanci a cikin sha’anin aure. Wanda daga shi ne ake iya hasashen ina auren ya nufa, ina zai iya kaiwa, kuma daga ina zai iya wargatsewa.
Wannan shi ya sa manya ba su cika yarda da kawai mutum ya zo sama ta ka su dauki yarsu su ba shi, ko kuma su su bar nasu dan ya dauko musu wata da ba su san komai game da gidansu ba.
Domin idan har aka ce mutum ya yi rashin sa’ar samun abokin zama, to fa wannan mutumin ya shiga wata rayuwa ce ta kunci, wadda idan ba tsananin dace ba, har a bada ba zai taba dawowa hayyacinsa ba.
Dukkan zabi kuwa da mutum zai yi, a matsayinsa na musulmi ko a matsayinta na musulma, to dole ne ya kasance bisa la’akari da koyarwa da shawara da kuma shiryarwa irin ta Annabi sallallahu alaihi wa sallam.
Na tabbata da yawan mu muna sane da cewa akwai nuni da aka yi ga maza kai tsaye cikin matar ko irin matan da su ka kamata su aura. Haka nan su ma matan akwai irin wannan nuni da aka yi musu.
Don haka ba mu da wata hujja da za mu ce mun afka rami ne bisa tsautsayi. Amma mu kalli me ya kore nutsuwa a cikin zaman aure tukun, kafin mu kara waiwayar wannan fanni.
Me Ya Hana Ma’aurata shisuwa?Daya daga cikin manyan dalilan kulla auratayya tsakanin maza da mata, kamar yadda mu ka ambata tun farko, shi ne samar da nutsuwa tsakanin mata da mijin.
Amma abin da da yawanmu, musamman matanmu ba su sani ba shi ne, nutsuwar mace tana `danfare ne da nutsuwar mijinta. kenan idan har shi namijin bai sami nutsuwa a gidansa ba, to tabbas wannan matar ma ba za ta taba samu ba.
Yayin da Ubangiji Mabuwayi ya nufi ambatar wannnan babbar manufa ta aure, sai Ya ce, a cikin Al Kur`ani mai tsarki:
“Shi ne (Allah) wannan da ya halicce ku daga rai `kwaya `daya (ran annabi Adam a.s). Sai Ya sanya wa wannan ran matarsa daga jikinsa.(Domin daga hakarkarin annabi Adam aka samar da matarsa Hauwa). Domin ya sami nutsuwa zuwa gare ta.
A wata ayar Ya ce:
“Kuma yana daga cikin ayoyinSa, Ya halitta muku matanku daga jinsinku (na mutane), domin ku rika samun nutsuwa zuwa gare su.
Sannan kuma ya sanya soyayya da jinkai a tsakaninku…”
ko kamar yadda ya ce Subhanahu wa ta`ala.
Kamar yadda za mu iya gani a wa`dannan ayoyi masu albarka guda biyu. Ana dangana samun nutsuwar ne ga namijin ko mazan.
Ba wai saboda nutsuwar macen ba ta da muhimmanci ba, sai don tabbatar da cewa samun nutsuwar matar yana da alaka ne da samun nutsuwar mijinta.
Wato yayin da duk namiji ya sami nutsuwa a gidansa, to fa tabbas wannan matar tasa za ta samu nutsuwa, haka kuma yayin da duk ya rasa nutsuwa ita ma duk `kulumbotonta ba ta isa ta samu ba.
Sai dai kamar haka ne kuma kan faru ga mijin da ya hana matarsa nutsuwa da gangan shi ma.
Kodayake, mutane da dama sukan yi tsammanin nutsuwa a inda kuma sam ba ta wurin.
Na sani watakila wasu su yi tsammanin samun nutsuwa a wurin matar da ta yi wasu `yan dabaru ta mallake miji tana juyawa tare da cutar da shi yadda take so. Ko mijin da ya karkarta ga matarsa `daya ba bar dayar tana cutuwa, da makamantan wadannan.
Maganar gaskiya ita ce, wadannan mutanen suna wata rayuwa ce irin ta `dan `baure, daga waje fes, amma zukatansu cike da damuwa. Don haka wadda duk da gaske take son nutsuwa a rayuwarta, ta bi hanyoyin samar wa mijinta nutsuwa.
Za mu dora a makon gobe insha Allahu.