- Tsohon shugaban rundunar soji, Laftanal janar Ipoola Alani Akinrinade, ya yi kaca-kaca da ma su sukar Buhari a kan batun rashin gabatar da takardunsa na karatu

Kazalika ya bayyana zargin Buhari da rashin yin karatu da cewar cin mutunci ne ga hukumar sojin Najeriya

- Ko a shekarar 2015 sai da wannan batu na bacewar takardun karatun Buhari ya jawo cece-kuce a tsakanin 'yan Najeriya

Tsohon shugaban rundunar soji, Laftanal janar Ipoola Alani Akinrinade, ya yi kaca-kaca da ma su sukar Buhari a kan batun rashin gabatar da takardunsa na karatu ga hukumar zabe mai zaman kanta.

Ko a shekarar 2015 sai da wannan batu na bacewar takardun karatun Buhari ya jawo cece-kuce a tsakanin 'yan Najeriya.

A wani jawabi da kakakin shugaba Buhari, Femi Adesina, ya fitar ya bayyana ma su yada zancen cewar Buhari bai yi karatu ba da marasa aikin yi.


©Image Legit

Jin haushin sukar da Buhari ke sha a kan rashin takardun ne ya saka Akinrinade alakanta batun batan takardun na shugaba Buhari da matsalar rashin iya adanai bayanai na hukumomi a Najeriya.

Shekara nawa kenan rabon Buhari da gidan soja?... shekara 50 kenan. Kowa ya san matsalar hukumomin Najeriya na rashin iya adana bayanai. Shin ma muna da ma'ajiya ta adana bayanai da takardu; ma'ajiyar da ke cike da beraye da Kyankyasai ," a cewar Akinrinade.

Kazalika ya bayyana zargin Buhari da rashin yin karatu da cewar cin mutunci ne ga hukumar sojin Najeriya.

© Legit.ng


Post a Comment

 
Top