Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana kula da duk wani motsi na rundunar yan sandan Najeriya yayin da rikici ke karuwa a kasar.
Ya kuma bukaci rundunar da ta kasance mai sanya idanu sosai wajen tsare garuruwa da kuma taka tsantsan wajen hukunta masu laifi.
“Rundunar yan sandan Najeriya ce gaba wajen tsare al’umma,Ta fannin shari’a babu abun da za su iya yi idan ba wai an kammala bincike bane.
“Daga yanzu, rundunar yan sandan Najeriya gwara ma ku lura da kyau, zan sanya idanu na sosai akan kum”inji shugaban kasar.
A baya mun kawo muku rahoton cewa Babban sufeto janar na ‘yan sanda, Mista Ibrahim Idris ya umurci dukkanin kwamishinonin ýan sanda da su kasance cikin shiri kan ayyukan mambobin kungiyar yan Shi’a.
A wata sanarwa daga kakakin, mukaddashin DCP Jimoh Moshood ya bayyana a Abuja a ranarTalata, 30 ga watan Oktoba cewa an umurci kwashinonin musamman masu fuskantar barazana daga ýan Shi’a da su dauki mataki akan su sosai kamar yadda doka ta tanadar.
“An bukaci su dauki mumunan mataki akansu daidai da doka sannan su hana yan kungiyar karya doka a jihohin,”inji shi.
Post a Comment