Wani tsoho dan shekaru 50, Ahamad Tijjani Muhammad, ya yiwa wata ‘yar karamar yarinya ‘yar shekaru 4 fyade garin Kano.

An gabatar da wanda ake zargi a gaban wata kotun Majistare da ke garin Kano.

An caji wanda ake zargi da laifin aikata laifin rashin tarbiya wanda ya sabawa sashe 285 na dokar Panel Code.

An bayyanawa kotun cewa mahaifin karamar yarinyar ‘yar shekaru 4, Yahaya Yakubu, ya mika karan lamarin zuwa ofishin ‘yan sanda da ke Sharada.


Post a Comment

 
Top