
Tsohon jigon siyasa a Nijeriya, tsohon ministan ayyuka kuma ginshiki a jam’iyyar
PDP tun daga kafuwarta, Cif Tony Anenih ya yi ajali bayan fama da rashin lafiya.
A watan Yulin wannan shekarar ne dai Cif Anenih ya soke taron bikin murnar cikarsa shekaru 85 da haihuwa bisa dalilin takaicin da halin kasar nan ke ciki na rashin daidaituwar al’amura.
A lokacin rayuwarsa, Anenih ya auti Madam Josephine Anenih, wata kwararriyar lauya wacce ta rike mukamin shugabar lauyoyi mata ta kasa tun daga shekarar 1994 zuwa 2000.
Haka kuma, mai dakin Anenih ita ta fara zama shugabar mata ta jam’iyyar PDP, daga shekarar 1999 zuwa 2005.
Za mu kawo muka karin bayani a nan gaba…
©Alummata
Post a Comment