A ci gaba da binciken abin da ya janyo faduwar jirgin saman kamfanin Lion Air a tekun kasar Indonesiya, masu aikin ceto sun gano na’urar tattara bayanan jirgin saman wanda ya yi hatsari kuma ya yi sanadiyyar rasa rayukan fasinjojin da yawansu yakai 189.
Da suke amsa tambayoyin manema labari kan samun na’urar bayanan jirgin saman masu binciken sun kara da cewar sakamakon binciken wannan hatsari zai kammala cikin wata daya yayin da sauran bayanai za su dauki watanni.
A shekara ta 2007 kasashen Turai sun haramtawa jiragen saman kasar Indonesiya sufuri a nahiyar Turai saboda fargabar rashin ingancin jiragen saman kasar.
Post a Comment