©fb image

Sharri 'Yan Sanda Suka Yi Mana, Ba Mu Kona Musu Mota Ba, Cewar 'Yan Shi'a
Daga Bilya Hamza Dass.

Mabiya Shi'a sun musanta zargin da jami'an tsaro ke musu na cewa sun koma wata motar 'yan sanda yau a yankin Wuse 2, bayan sun tashi daga wani gangami da suka shirya a garin Abuja.

image copyright facebook

©fb image

Wakilin Shaik Zakzaky na garin Kano Dakta Sunusi Abdulkadir yana daga cikin wadanda suka jagoranci gangamin ya bayyanawa manema labarai yau cewa ba su da masaniya da wannan aikin yana me cewa “mune aka kashe aka kama wasun mu aka ji mana raunuka bayan mun fito bayyana kiranmu akan a sake mana Malaminmu.

Ya kara dacewa “muna masu nisanta kanmu da wannan aiki kuma muna zargin jami'an tsaro sun yi haka ne domin gogawa wannan harkar kashin kaji”


Post a Comment

 
Top